"Liverpool zata iya baje Barcelona daci 4-0 a wasan yau"

Tauraron dan kwallon Manchester City, Ilkay Gundogan Yace yana da yakinin Liverpool zata iya yin nasara akan Barcelona a wasan zagaye na biyu na neman cin kofin Champions League da zasu buga da yammacin yau.


Liverpool dai tasha kashi a hannun Barca a zagayen farko da ci 3-0, wanda Suarez da Messi suka ci, sannan a wasan yau babu taurarin masu ci mata kwallo biyu, Mohamed Salah da Roberto Firmino, sannan tana bukatar kwallaye 4 kamin ta yi nasara akan Barca, idan Barca din bata kara saka kwallo a ragarta ba kenan.

Da yake magana da DAZN, Gundogan yace, wasan yau fa be kare ba domin komai na iya faruwa. Liverpool zasu iya cin 4-0 a wasan na yau, yace idan aka zo Anfield Klopp na zama inji me zaburar da 'yan wasa wanda kwata-kwata ba kanwar lasa bane kuma zasu iya gamawa da Barca.

Post a Comment

0 Comments