Trump ya taya Musulmin duniya zagayowar watan Ramadhan

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya taya Musulman kasarsa da na duniya baki daya murnar zagayowar watan Azumin Ramadhana mai alfarma.


A wata rubutacciyar sanarwa da Trump ya fitar ya fadi cewar "Ni da Melania muna taya dukkkan Musulmi murnar zagayowar wannnan wata mai albarka."

Trump ya tunatar da cewar a watan Ramadhan ne aka saukar da Alkur'ani Mai Tsarki ga Annabi Muhammad (SAW) kuma bayan ganin jaririn wata Musulmai suna fara ibadar azumi tare da sabunta imaninsu, wanda hakan ke kara musu daraja da martaba.

Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa, a watan Ramadhan Musulmai na azumi, na karanta Alkur'ani, suna taimakon marasa karfi wanda hakan ke ba su damar godewa Allah tare da ssamun Rahamarsa.

Ya ce, "a wannan wata za su kara karfafa alakarsu da dangantakarsu da Musulmai, wannan babbar dama ce ta samun ni'ima da kuma kara daukakar mu a matsayin abokai zuwa mataki babba."
TRThausa.

Post a Comment

0 Comments