dan Allah a daina daukar hotuna ana sakawa a yanar gizo idan an bayar da sadaka__Nazir Sarkin Waka

nazir sarkin waka

shahararren mawakin hausannan kuma sarkin wakar sarkin kano wato Nazir M Ahmad ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na sada zumunta na instagram inda yake cewa acikin bidiyon:
ba cewa nayi kada ayi sadaqa ba abun da na ke cewa shine idan anyi a daina daukan hoto ana sakawa a shafukan sada zumunta,idan mutum yayi ya dauki hoton sai yabarsa acikin wayarsa yana kallo yanajin dadi.
yacigaba da cewa riya na iya shigowa ciki,kuma idan riya bata shigo ba zalinci zai iya shigowa ciki tunda zaka dauki hoton mutum kaje kana tallan gidauniyarka,neman kudi.
Yace saka hoton mutum cin fuskane,
domian kallon bidiyon sai kudanna bluen rubutun dake kasa.
danna nan
 yace misali ace sai kaga hoton mahaifiyarka tazo an bata sadaka a shafin yanar gizo,ya zaka ji? Akwai mutane dake son zuwa su karba amma saboda gudun tonon asirin da za'a musu sun kwammace su kwana da yunwa.

Ya kara da cewa idan kana takamar kana raba buhu goma ko sama da haka to akwai me raba buhu dubu amma baya irin wannan abu,kuma ba kaza ba zuma ko kilishi kake rabawaba amma kake wannan abu.

Post a Comment

0 Comments